Duk wani tababa da ake yi gameda baban zabe a Nigeria ya kau, domin Majalisar kasa ta cimma wannan matsayi bayan ta kwashi sa'o'i kusan tara tana gudanar da taro akan kiraye kirayen da wasu ke yi cewa a dage yin zabe.
Wasu sun bada hujjar cewa hukumar zabe bata gama shiri ba, Wasu kuma cewa suka yi a saboda hare haren da yan kungiyar Boko Haram ke kaiwa.
To amma kudurin na taron Majalisar kasa ya biyo bayan tabbacin da shugaban hukumar zabe Professor Attahiru Jega ya baiwa Majalisar, inda yace hukumar zabe, a shirye take ta gudanar da zabe.
Wakiliyar sashen Hausa Medina Dauda taji ra'ayin wakilan jam'iyar APC mai hamaiya da kuma jam'iyar PDP wadda take jan ragamar mulki.