Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Justin Welby Ya Yi Murabus A Matsayin Babban Limamin Canterbury


FILE - Archbishop of Canterbury Justin Welby stands at Westminster Abbey ahead of the coronation of King Charles III and Camilla, the Queen Consort, in London, May 6, 2023.
FILE - Archbishop of Canterbury Justin Welby stands at Westminster Abbey ahead of the coronation of King Charles III and Camilla, the Queen Consort, in London, May 6, 2023.

Babban Limamin Canterbury Justin Welby ya bayyana haka ne yayin wani taron addu’o’i da tuntuntuni.

A yau Talata, Archbishop Na Canterbury Justin Welby, kuma babban limamin cocin Ingila, ya yi murabus cikin alhini, inda yace ya gaza wajen tabbatar da an gudanar da cikakken bincike akan zarge-zargen yin lalata da wani sansanin kiristoci ‘yan sa kai yayi shekaru da dama da suka wuce.

Welby, wanda ya kasance jagoran addini ga Kiristoci mabiya darikar Anglican milyan 85 a fadin duniya, ya fuskanci kiraye-kirayen yayi murabus bayan da wani rahoto da aka fitar a makon daya gabata ya gano cewar ya gaza daukar matakan da suka dace wajen takawa mutumin da za’a iya cewar shine wanda aka fi samu da laifin yin lalata da mutane da dama a tarihin cocin.

A cikin takardar yin murabus din tasa, Welby yace wajibi ne “ya dauki laifin gaza daukar mataki a kan wadannan munanan laifuffuka “da kansa dama a hukumance.”

Babban limamin yankin York Stephen Cottrell, mutum na biyu mafi girman mukami a cocin, ya kira murabus din Welby da “abu mafi karamci da dacewa”.

Akwai yiyuwar majami’un Anglican na kasashen nahiyar Afirka irinsu Uganda da Najeriya su yi murna da murabus din Welby, bayan da a bara suka ce sun deba kauna akansa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG