Starlink, bangaren tauraron dan adam na tashar sararin samaniyar “SpaceX”, na aiki a kasashen nahiyar Afrika da dama sai dai ya fuskanci kalubalen bin ka’idoji a wasunsu da turjiya daga kamfanonin sadarwar kasashen da suka mamaye harkar.
“Mun jima muna tattaunawa da Starlink tun a 2021 kuma mun amince akan muhimman batutuwa,” kamar yadda ministan sadarwar chadi Boukar Michel ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters ta wayar tarho.
Alkaluman bankin duniya na baya-bayan nan sun nuna cewa kaso 12 cikin 100 ne kacal na al’ummar Chadi ke da damar amfani da intanet a 2022.
“Bamu karade galibin yankunan kasarmu da wayoyin sadarwar “fibre optics” da ake birnewa a karkashin kasa ba, kuma na yi imanin cewa na’urar Starlink za ta bamu damar cike wannan gibi,” A cewar Michel, inda ya kara da cewa ingantacciyar sadarwar intanet za ta baiwa Chadi damar zamanantar da ayyukan gwamnati a wurare masu nisa tare da bunkasa sabbin sana’o’in dake da nasaba da fasahar zamani.
Elon Musk ya wallafa a shafinsa na X a jiya Litinin cewar “akwai na’urar Starlink yanzu haka a Chadi”.
Kamfanin sadarwar intanet din na aiki a kashashen Afrika da dama ciki har da Zimbabwe da Najeriya da Mozambique da Malawi da Madagascar da Jamhuriyar Benin da Sudan ta Kudu da Eswatini da kuma Saliyo.”
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna