Sai dai wadanda suka tsira daga harin ciki har da ma’aikatan agaji, sun jajirce cewa, an kwashe sa’oi biyu ana kai hari akan jerin manyan motocin kayan agaji 31, daga jiragen yaki ko kuma jirage masu saukar ungulu, inda suka yi amfani da makamai masu linzami.
Daga cikin wadanda suka ba da shaida, har da wani jami’in hukumar ba da agaji ta Red Crescent, wanda shi aka dorawa alhakin kula da motocin.
Ali Barakat, wanda shima ma’aikacin agaji ne, ya ce, ya kwanta a kasa ne a lokacin da aka fara kai harin, amma kuma kaninsa Omar Barakat wanda ke da ‘ya’ya tara bai tsira ba.
Barakat ya fadawa manema labarai cewa, fiye da makamai masu linzami 20 ne suka fada akan ayarin motocin a daren Litinin a kusa da garin Uram-al Kubra.
Kungiyar ba da agajin ta Red Cross, ta ce akalla fararen hula 20 aka kashe a harin, wanda jami’an Rasha su ka ce ‘yan aawaye ne suka kai, ba dakarun kasar ba.