Bayan dimbin matrakan da Amurka da Rasha suka sha dauka na karya ka’idojin wannan yarjejeniyar a Syria, a farko farkon wannan wata, musamman harin baya-bayan nan na jiragen sama da aka kaiwa ayarin ayarin motocin dake dauke da kayan agaji a ranar Litini wanda Amurka ta zargi Rasha, Kerry yace dukan bangarorin biyu suna fuskantar lokaci na fadar gaskiya.
Kerry dai yayi anfani da lafazin diplomasiya inda bai ware bangare daya na Syria ko Rasha don dora musu laifin kai farmakin ba, duk da cewa sune ake zargi da laifin kai galibin duk hare haren da aka kai a yankunan fararen hula, wanda kuma ya janyo mutuwar mutane da dama.
To amma Ministan harkokin wajen Rasha Serigei Lavrov da yayi jawabi a taron kwamitin sulhun kafin Kerry, bai gaggauta mayar da martini a kan shawarar Sakataren harakokin Wajen Amurkar ba, sai dai daga bisani wata mace mai Magana da yawunsa tace shawarar Amurkan holoko ne kawai.