Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tashin Wani Bom A Syria Ya Kashe Ma'aikatan Agaji Dayawa


Wani babban jami’in hukumar agajin gaggawa na MDD, yace an tada bam kan wani ayarin motocin hadin guiwan MDD da kungiyar Red Crescent ta Syria a jiya Litini a birnin Aleppo dake yammacin Syria, da ya kashe ma’aikatan kai kayan agaji da dama, wadansu kuma suka jikata.

Wani mashawarcin MDD na musamman Jan Egeland , da yake jawabi da yammacin jiya, yace ayarin motocin na dauke da kayan agajin gaggawa na mutane kusan dubu tamani ,sai dai bai yi Karin bayani a kan rasa rayuka da kuma rauni da aka samu ba.

Masu fafutuka da ake dangantawa da yan adawa Syria, sun ce kimanin ma’aikatan kai agaji 12 da wasu direbobin roka ne aka kashe a wannan harin, jim kadan bayanda Syria ta ayyana karshen tsagaita wuta na mako daya.

Izuwa yanzu ba a iya gano jirgin wanene ya kai wannan farmakin a kan motocin ba. Sai dai nan da nan ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon tace rudunar hadin guiwa karkashin jagorancin Amurka bata da hannu a ciki.

An bukaci kulla yarjejeniya ce don bada daman shiga da abinci da magunguna ga dubban daruruwar fararen hula a Syria da basu samun agaji daga rundunar gwamnatin kasar.

Ko da yake masu sa ido na ma’aikatar agajin sun ce babu wani kayan agaji da aka raba a kwanakin shidan farko na yarjejeniyar, a yayinda suka dora laifi kan gwamnatin shugaba Bashar al-Assad da bijirewa yarjejeniyar, ta wajen hana daman kai kayan agajin.

Da safiyar jiya Litini, jami’an Amurka sun ce wakilai daga kasashe 19 masu aikin agaji a Syria zasu yi wani zaman tattaunawar gaggawa a yau Talata a helkwatan MDD da nufin bayyana halin da ake ciki a kasar Syria da yaki ya daidaita.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG