Kungiyar Kasa da Kasa ta Taimaka Ma Siriya mai mambobin kasashe da kungiyoyi 20 (ISSG a takaice), ta yi taro na tsawon kimanin sa'a guda jiya Talata a birnin New York, ta kuma yanke shawarar kara taro ranar Jumma'a.
"Yarjajjeniyar tsagaita wutar ba ta mutu ba," abin da Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry ya gaya ma menama labarai kenan, yayin da ya ke fitowa daga taron na ISSG.
An yi imanin cewa tsakanin Siriya da Rasha wata ta kai harin jiragen sama kan tawagar motoci 31 na dakon kayan agaji da ke dosar birnin Alepo na kasar Siriya daga kan iyakar Turkiyya. Harin ya rutsa da 18 daga cikin motocin, ya kuma hallaka farar hula 20 da kuma shugaban kungiyar agaji ta Red Crescent ta yankin, a cewar kungiyar.