Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kasa Ceto Mutane Akalla 7 Da Motar Da Suka Nutse a Ruwa


Mota ta nutse a ruwa tare da mutane akalla bakwai.
Mota ta nutse a ruwa tare da mutane akalla bakwai.

Iyalan mutanen da suka fada gada a cikin motar safa suna zaman zullumi bayan sun wuni sun kwana a ruwa ba a fitar da su ba.

Wani shaidan gani da ido mai suna Alhaji Yaro, ya fadawa Muryar Amurka cewa, motar ta fasinja mai dauke da mutane akalla 7, ta tashi ne daga Sokoto da misalin karfe 10 na safe agogon Najeriya zuwa Kware, inda ta kwace ta fada ruwa ta kuma nutse, tare da makalewa a wata gada da ake kira ‘Gadar Zazzalo’ da ke kan kogin Rima, kuma dukkan mutanen ba wanda ya sami fita daga motar.

Rahotanni sun bayyana cewa dukkan hukumomin tsaro da na agaji na gwamnatin jiha da na tarayya sun sami isa wurin daga baya, to amma duk sun kasa fitar da motar da mutanen da ke cikin ta.

Motocin 'yan kwana-kwana a wajen da motar ta nutse cikin ruwa
Motocin 'yan kwana-kwana a wajen da motar ta nutse cikin ruwa

Daga bisani dai an nemi masunta da masu ninkaya na gargajiya, wadanda su kuma suka ce sai in za’a biya su ne kawai za su shiga ruwan.

“Nan wurin aka sami roba aka yi baran tarbace tsakanin jama’ar da suka taru, insa aka sami tara Naira 8,000, to amma masuntan nan suka yi tsaye lallai sai an ba su akalla Naira 20,000,” in ji Alhaji Yaro.

Ya ci gaba da cewa “an kuma yin zagaye na biyu na meman tarbacen aka sami karin kudi a daidai mutane na kara taruwa a wajen, to amma daga karshe masuntan nan suka shiga suka kuma fito a haka, suna cewa motar ta makale kuma sun kasa ko da bude ta saboda karfin ruwa.”

Masuntan gargajiya da masu ninkaya na kokarin gano inda motar ta makale a cikin ruwa
Masuntan gargajiya da masu ninkaya na kokarin gano inda motar ta makale a cikin ruwa

Shugaban masuntan, Mai Tarun Sarkin Jirgin Sarkin Musulmi Muhammadu Sada ya fadawa wakilinmu cewa “hakika mun shiga mun kuma ji inda motar take, amma abin da ke cikinta, Allah kadai ya sani ko akwai mutane ko babu.”

Jami’an ‘yan kwana-kwana na jihar Sokoto da ma na gwamnatin tarayya, kazalika da na hukumar agaji ta kasa wato NEMA, duk sun hallara a wajen amma ba’a sami shiga ruwan ba balle a fitar da mutanen har ya zuwa faduwar rana.

Kwamandan hukumar kashe gobara ta kasa mai kula da yankin Sokoto, Mohammed Jibrila, ya ce sun yi iya kokarin su amma dai ba su kai ga nasara ba tukunna.

“Da ma irin wannan aiki ne da ya hada hukumomi da dama, inda kowa zai yi abin da zai iya domin a ga an cimma makasudin da ake son cimmawa. Saboda haka sai gobe da safe za mu sake dawowa tare da taimakon wasu kamfanonin da za su taimaka mana a wannan al’amari,” in ji kwamanda Jibrila.

Hakan na nufin kenan motar da mutanen da ke cikin ta za su kwana a cikin ruwan, bayan sun wuni ba’a san yanayin da suke ciki ba.

MOotocin 'yan kwana-kwana a wajen da motar ta nutse cikin ruwa
MOotocin 'yan kwana-kwana a wajen da motar ta nutse cikin ruwa

Mai sharhi akan lamurran yau da kullum, kuma shaihin malami a jami’ar Usmanu Danfodiyo ta Sokoto Farfesa Bello Muhammad bada, ya ta’allaka wannan yanayi da rashin horo da kayan aiki ga hukumomin gwamnati na ceton rayukan jama’a.

“Kana gani a wasu kasashe rayuwar mutum daya tana da matukar muhimmancin, kuma akan ceto rayuwarsa, sai ka ga kasar kamar za ta je yaki ne. Mu ko a nan (Najeriya) kullum kana gani masifu na zuwa amma ba abin da ake yi,” a cewar Farfesa Bada.

Ya zuwa lokacin wallafa wannan labarin dai ba’a kai ga tsamo motar ba, haka kuma ba’a san halin da direba da fasinjojin suke ciki ba. To sai dai rahotanni sun ce an girke sojoji a wajen da lamarin ya auku da yammacin ranar Alhamis, domin su sanya ido kafin wayewar garin ranar Juma’a a ci gaba da kokari.

Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00




Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG