Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Fashin Teku Sun Yi Awon Gaba Da Ma'aikatan Wani Jirgin Ruwa


'Yan Fashin Teku sun yi awon gaba da ma'aikatan jirgin ruwa, jim kadan bayan sun bar Najeriya.

Wasu 'yan fashin Teku sun yi awon gaba da ma'aikatan jirgin ruwa a gabar Tekun Guinea har su 15, wanda suka kwashe kimanin sa'o'i 6 don su kama mutane da zummar yin garkuwar da su. Lamarin dai ya faru ne a daren Asabar 23 ga watan Janairu. Daya daga cikin ma'aikatan jirgin ya rasa ransa.

Gwamnatin jamhuriyar Turkiyya, ta rubuta a shafinta na twitter cewar, shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan, ya samu ganawa da daya daga cikin matuka jirgin da 'yan ta'addan basu tafi da shi ba, ya kuma sanarwa shugaba Recep cewar 'yan fashin sun basu kashi kamun suka tafi da wasun su.

Lamarin dai ya faru ne jim kadan bayan jirgin ya bar tashar jirage da ke Ikko a Najeriya, akan hanyar sa ta zuwa birnin Cape Town da ke kasar Afrika ta Kudu. Ya zuwa yanzu dai gwamnatin Turkiyya ta shirya sojojin kundunbala na musamman don suje farautar 'yan fashin.

Ana kuma sa ran zasu yi shawagi da har zai kai su nahiyar Afrika, don ganin sun kubutar da ma'aikatansu. Rundunar sojojin ruwan Najeriya dai basu ce komai akan lamarin ba.

A tashi fahimtar tsohon shugaban kungiyar Kwadago ta Najeriya, Kwamrade Isah Tijjani, yana ganin cewar babu abun mamaki akai, don kuwa ko a shekarar 2000 zamanin gwamnatin Obasanjo an yi ta kira cewar a kafa kungiyar tsaron ta ruwa ta kasashen Afrika, da nufin kawo karshen irin wadannan matsalolin.

Gabar tekun Guinea dai ita ce mafi hadari a duniya a cewar kungiyar kula da sufurin ruwa ta Duniya.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina a cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG