Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bakin Haure 3 Sun Mutu Bayan Da Wani Jirgin Ruwa Ya Kama Da Wuta


Masu aikin ceto a lokacin da suke dauke wata gawa daga cikin jirgin ruwan
Masu aikin ceto a lokacin da suke dauke wata gawa daga cikin jirgin ruwan

‘Yan sandan Italiya sun ce bakin haure akalla uku ne su ka mutu, shida su ka jikkata, daya kuma ya bace, bayan da karamin jirgin ruwan da ke dauke da su ya kama da wuta a tekun Ionian.

Bidiyon masu tsaron gabar teku ya nuna jirgin ruwan na ci da wuta yayin da masu ayyukan ceto ke ta gaya ma mutanen cikin jirgin abin da za su yi, da murya mai karfi, lokacin da suke kokarin ceto su daga cikin tekun.

‘Yan sanda sun ce injin din jirgin ne ya kama da wuta ya kuma yi bindiga, yayin da jirgin ke kokarin shiga gabar tashar jirgin ruwa. Ba a san takamaiman adadin mutanen da ke cikin jirgin ba.

Kafafen yada labarai sun ce akwai mutane 21 cikin jirgin lokacin da ya kusanci gabar, kuma ‘yan sandan Italiya sun tasa keyar 13 daga cikinsu, tun kafin ma jirgin ya kama da wuta.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG