KADUNA, NIGERIA - An dade dai ana samun sabani tsakanin Malamai game da wurin daukar haramar aikin hajji wato Mikati da wasu bangarorin aikin hajjin da a wani lokacin hakan kan rikitar da sabbin alhazai, shi ya sa hukumar kula da jin dadin maniyyata ta Jihar Kaduna ta fitar da sabbin tsare-tsare, kamar yadda shugaban hukumar, Dr. Yusuf Yakub Arrigasiyyu ya shedawa Muryar Amurka a lokachin taron bita kan wadannan tsare-tsare.
Ya ce daga yanzu alhazan jihar Kaduna, a Mikati daya za su rinka daukar niyya kuma malaman da za su yi wa maniyyata bita ma sai hukumar ta tantance su.
Manyan malaman da su ka halarci taron sun ce sabbin tsare-tsaren za su taimaka wa maniyyata sai dai kuma wasu ka iya yunkurin bijirewa tsarin.
Cikin sabbin tsare-tsaren da hukumar kula da jin dadin alhazan jahar Kadunan ta fitar dai har da shiga jigilar masu aikin Umara, in ji shugaban hukumar Dr. Yusuf Yakub Arrigasiyyu.
Wannan ne dai karo na farko tun bayan dage takunkumin zuwa Saudiya saboda cutar Korona, da ake sa ran kasashe za su yi jigilar maniyyata masu yawa kamar yadda aka saba kafin bayyanar cutar Korona.
Saurari cikakken rahoto daga Isah Lawal Ikara: