WASHINGTON, D.C. - "Za mu iya tabbatar da cewa tayin da kawarmu Faransa tayin, cikin gwargwadon ikon da ake da su, na daukar 'yan Jamus a cikin jiragensu daga Nijar," in ji ma'aikatar a cikin wata sanarwa, ta kara da cewa ta shawarci "dukkan Jamusawa da ke Yamai da su amince da hakan."
Tuni dai aka rufe iyakokin saman Nijar ga jiragen ‘yan kasuwa bayan hambarar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum da zababben gwamnatinsa ta dimokradiyya a ranar Larabar da ta gabata.
Faransa na shirin kwashe daruruwan Faransawa da turawa daga Nijar cikin sa'o'i 24 masu zuwa. Gwamnatin Jamus ta ce a ranar Litinin din nan ba ta shirya kwashe 'yan kasarta ba bisa la'akkari da halin da ake ciki.
Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta fada jiya Litinin cewa tana kyautata zaton 'yan kasar Jamus kasa da 100 ne a halin yanzu a Nijar, ban da wadanda ke cikin kasar a wani bangare na rundunar sojin Bundeswehr.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna