Yinkurin wasu ‘yan Majalisar Dattawa ‘yan APC na zaben dan takarar Shugaban Majalisar Dattawa kamar yadda ‘yan’uwansu ‘yan APC a Majalisar Wakilai su ka yi, ya ci tura, saboda wasu Sanatoci kimanin 65 sun yi watsi da yinkurin da cewa ya saba ma tsarin dimokaradiyya. Wannan, kamar yadda wakilinmu a Abuja Nasiru Adamu Elhikaya ya lura, na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin zaben Shugabannin Majalisar Tarayyar Najeriya.
Elhikaya ya ruwaito Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura na cewa su da ke so a shiga a yi zabe kamar yadda tsarin dimokaradiyya ya tanada sun gana da masu son a dora wani mutum guda, inda su ka nuna masu cewa su fa za su bi tsarin na dimokaradiyya.
Haka zalika, Sanata Danjuma Goje, wanda ya ce ko Shugaba Muhammadu Buhari ma ya ce a bi tsarin da ke shimfide, ya ce shi ma ya na ra’ayin kowa tasa ta ficce shi – ma’ana a je a buga mai rabo ya dare kujerar Shugaban na Majalisa.
Idan za a tuna dai, a gabanin zaben Kakakin Majalisar Wakilai na 8, wanda za a yi ranar Talata,jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta zabi Femi Gbajabiamila wanda ya fito daga Lagos a matsayin dan takararta, a cikin wani yanayi mai tattare da takaddama , da kauracewa.