A jawabin da sanata Barnabas Gemade yayi a taron manema labarai wanda yake bayyana tsarin da aka bi wajen zaben Dakta Abubakar Bukola Saraki a matsayin shugaban majalisar dattawan Najeriya a matsayin haramtacce, saboda haka ba zai iya samun wani halacci ba saboda zasu garzaya kotu.
Sai dai kuma za’a iya cewa an sami baraka a batun zuwa kotun domin sanata Bukar Abba Ibrahim tsohon gwamnan jihar Yobe, kuma jihar da Dakta Ahmed Lawal din ya fito ya bayyana wa wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina cewar shi kam sam baya goyon bayan zuwa kotun.
Wakilin Muryar Amurka ya tambayi sanata Bukar Abba Ibrahim cewar tun da yace Bola Tinibu ne ya rarrashe shi da ya bi bayan Dakta Ahmed Lawal, kenan ra’ayoyin wasu ‘yan Najeriya cewar Tinibun ne yake son juya yadda zaben majalisar zai kasance ya tabbata gaskiya, inda ya rantse da cewar Tinibu bai taba sanin Ahmed Lawal ba siyasa ce kawai ta kawo ya ga mutane ne suke sonsa, kuma babu wani da abinda ya hadasu.