Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kallo Ya Koma Majilisun Dokokin Tarayyar Najeriya


Tsoffin gwamnoni da wadanda suka shiga a waren PDP da suka shiga gamayyar APC.

Magoya bayan masu neman shugabancin shugaban majilisar dattawa dana wakilai na shigowa cikin Abuja domin shedawa wannan zaben da za a yi zauren majilisun baya ga yan takaran jamiyyar APC sanata Ahmed Lawal a majilisar dattawa da Femi Gbajabiamila a wakilai magoya bayan masu adawa da matsayin na karfafa wa gwanayen nasu gwiwa na nuna barin zaben shine zai karfafa demokaradiyya.

‘’Sunana Honarabul Yakubu Aliyu na tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar Das a jihar Bauci tun dagaBauci muka taso domin mu zo mu gwada wa dan uwan mu goyon baya sabo da mutun ne wanda yake son ci gaba, mutum ne wanda ba ruwan sa da banbancin addini, Buhari yace a bari aje ayi zabe mu idan an kada dogaramun tabbatar an kada shi ne zamu dauki kaddara’’.

Tsoffin gwamnoni da wadanda suka shiga a waren PDP da suka shiga gamayyar APC na mara baya ga Bukola Saraki don jagorantar dattawa, a kaikaice dai suna zargin uban jamiyyar Bola Tinubu nason nada mukarabban sa ne a manyan mukamai ga dai abinda tsohon gwamna Sani ke cewa.

‘’Tunda ana son a tilasta kana ji shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari ya fito karara yace wa duniya baida raayi baida shaawa ga wani dan takarar sa, me yasa yayi haka domin yaji ana yawo da sunan sa ana cewa ga wanda yake so ga wanda baya so, su kuma wadannan da suke kokarin yin hakan kowa yasan su duk Najeriya na tabbata insha Allahu an san su dama haka suka saba siyasa saboda haka muke son mu nuna musu cewa siyasa ta canza a jamiyyar APC jamiyya ce ta al’umma baki daya ta Najeriya kuma insha ALLAHU ALLAH yafi sanin zukatan mu gurin mu shine muga cewa mun taimakawa wannan bawan ALLAH ya sauke nauyin da ALLAH ya dora mashi, kuma mu kammu ALLAH zai tambaye mu’’

Ibrahim Abdulkarim na ofishin goyon bayan Buhari na ganin shugaban kasa ya nuna cika alkawarin sa na rashin tsoma baki a lamurran majilisa.

‘’ Yanzu me ya iya taimako irin taimakon da shugabankasa yayi na cewa ya barsu suyi yanzu da wasu suka sa baki ba kuga yadda abin ya kara zafafa ba ya kara zama rigima da shima yasa bakin sa tun lokacin nan da yanzu abin ya zama rigima, amma sabo da zaman shi da irin tunanen sa da irin hangen nesan da yake dashi yace ya cire hannun shi, da suma sauran manyan sun yi yadda yayi suka bi misalign sa da ba za a samu ba, Ina kuma kira gare su wannan mutumin ALLAH ne ya kawo shi su rika ganin musalai da yake kawo wa idan suka bi irin musalan sa ba zamu sha wahala ba’’

Sai an gudanar da zaben ne amma ba a a iya cewa ga wanda zai lashe zaben dake cike da sarkakiyya.

Kallo Ya Koma Majilisun Dokokin Tarayyar Najeriya - 3'00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:14 0:00

XS
SM
MD
LG