Kokarin da jam'iyyar APC tayi na sasanta 'yan takarar shugabancin majalisar dattijai data wakilai ya faskara.
Sakamakon zaben 'yar cikin gida da shugabannin jam'iyyar suka gudanar, ya nuna cewa Femi Gbajabiamila, ya sami nasara. Amma Yakubu Dogara, ya bayyana cewa zaben da wakilan majalisar baki daya zasu yi ranar talata ne kadai zai amince da shi.
Magoya bayan Dogara suka ce yaya jam'iyya zata yi amai ta lashe, tace ba zata tsoma baki ba, yanzu kuma shugabanni su fito suce ga yadda za'a yi, ba dai dai bane.
Wasu suka ce ai "ba'a fafe gora ranar tafiya", muddin kuwa aka yi haka, tilas wanda ya fafe goran yasha ruwa mai daci.
Yanzu dai an dare gida biyu a majalisun duka biyu, a gefe daya akwai Femi Gbabiamila wanda jam'iyya ta fitar, zai kara da Yakubu Dogara, wanda yaki amincewa da hukuncin jam'iya, a majalisar dattijai kuma, Ahmed Lawal ne dan takararda jam'iyya ta fitar, yayinda Bukola Saraki, yace bai yarda ba zaiyi takara.