Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an 'Yan Sandan Zambiya Sun Musanta Zargi


Jami’an ‘yan sandan kasar Zambia sun fito ‘karara sun musunta rahotannin da aka fitar a kasar dake cewa sun kame wasu ‘yan kasashen waje, dalilin kada kuri’a da sukayi a babban zaben jin ra’ayin mutane da kuma babban zaben ‘kasa.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Zambia, Rae Hamong, shima ya fadawa Muryar Amurka cewa angudanar da zabe lafiya, sai dai ‘yan rigingimu da ba za a rasa ba. ‘yan sanda sun tabbatar da tsaron da ake bukata wajen gudanar da zaben.

Ya ‘kara da cewa “A yanda ‘yan sanda ke dauka, rahotannin basu da sahihanci kamar yadda bayananmu ke nunawa, babu wani rahotan da ke cewa an kama wani ‘dan ‘kasar waje ba.” ya ci gaba da cewa kofar mu a bude ta ke, idan wani yana da bayani haka zai iya tuntubar mu, kuma za a binciki lamarin.

Hamong yace ‘yan sandan da aka aika runfunan zabe a fadin kasar kwararru ne an basu horo tabbatar da cewa masu jefa kuri’a sun yi zabe kamar yadda tsarin mulki ya basu dama ba tare da tsoron an ci zarafin su ba.

Kungiyoyin kare hakki da ta addinai sun nuna damuwarsu kan tashe tashen hankula lokacin kamfe din zaben. Bayan da magoya bayan jam’iyyar mai mulki ta Patriotic Front da jam’iyyar adawa ta United Party for National Development UPND a takaice, suka zargi junansu da tayar da zaune tsaye da kuma yagawa junansu hotunan ‘yan takara da ake likawa.

Sai dai ‘yan sanda sunce sun cafke mutanen da ke da hannu a tashin hankalin. Duk da cewa ana zargin ‘yan sanda da nuna son rai ga jam’iyyar PF mai mulki.

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG