Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Libiya Sun Karya Lagwon ISIS


Dakarun Libiya da suka cafke hedkwatar ISIS a Libiya suke murna
Dakarun Libiya da suka cafke hedkwatar ISIS a Libiya suke murna

A Libya, dakarun gwamnatin kasar sun bada labarin cewa sun kama helkwatar ISIS dake birnin Sirte.

Wannan bayanan yana kunshe ne cikin wata sanarwa da dakarun dake biyayya ga gwamnatin hada kan kasar ta ftar.

Helkwatar tana wani sanannin gini mai tarihi a garin wanda nan ne mahaifar tsohon shugaban kasar na kama karya Moammar Gaddafi, da kungiyar ta ISIS take amfani da shi domin tarurruka da karantawar addini, bayan suka kama iko kan garin a bara.

Amurka tana kai hare hare da jiragen yaki da zummar tusa keyar 'yan kungiyar daga binrin na Sirte dake kan gabar teku,wanda suke amfani da shi a zaman cibyar tafiyarda harkokinsu.

Jami'an Amurka sun jaddada jiya Laraba cewa, sojojin kasa na Amurka basa gudanar da yaki kai tsaye a fafatawar da ake yi.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG