Sai dai kuma wannan zanga-zangar na iya kawo manya-manyan kabilun kasar waje daya domin kuwa sun ce abu guda ke damun su.
Wannan ne yasa wasu masu kula da al’amurran yau da kullun ke cewa ba mamaki a sake samun wani sabon tashin hankali a kasar
Yanzu haka dai kusan mutane 100 aka kashe kuma jami’an tsaro ne suka auka masu suka murkushe wadannan masu zanga-zangar a cikin karshen satin daya gabata.
Jamiyyar adawa ta kasar ita da kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesaty International suka ce jami’an tsaro sun bude wa masu zanga-zanga wuta, abinda yayi dalilin mutuwar wasu daga cikin su.
Gwamnatin kasar ta Habasha tace wannan ba laifin kowa bane illa na ‘yan adawa domin ko sune suka shirya zanga-zanga bada neman izinin yin hakan ba.
Mai Magana da yawun gwamnatin kasar yace masu zanga-zangar wasu daga cikin su na dauke da makamai ciki ko harda bamb.
Sai dai ‘yan adawa sunce wannan zuki ta mallaki ce masu zanga-zangar basu dauke da kowane irin makami kuma suna gudanar da zanga-zangar su cikin lumana.