Tsoffin jami’an dai sun nuna goyon bayansu da kira ga majalisar dinkin duniya ta aika sojojin kiyaye zaman lafiya domin kawo karshen tashin hankalin da ake fama da shi a kasar. Jakadan Sudan ta Kudu a nan Amurka Gordon Buay, wanda ya jagoranci wani taron ‘yan kasar Sudan ta Kudu dake zama a kasashen waje, ya kira duk wani ‘dan Sudan ta Kudu da ke kira ga majalisar dinkin duniya da ta karbi ikon kasar a matsayin maci amanar kasa.
Yace “ Duk wani ‘dan ‘kasar da ke rike da fasfo ‘din Sudan ta Kudu, ya shiga layin masu kira ga majalisar dinkin duniya ta karbi ikon ‘kasarsa to yakamata a kwace masa fasfo.”
Bayan da aka shaida masa cewa a dokar Sudan ta Kudu babu inda aka haramta cewa ‘yan Sudan ta Kudu dake zaune a kasashen waje kar su fadi ra’ayinsu, Buay dai maida martani inda yace laifi ne a kotun Sudan ta Kudu.
A jiya Alhamis ne ‘yan kungiyar Sudan ta Kudu dake a kasashen waje, sukayi maci ta kofar hedikwatar majalisar dinkin duniya dake birnin New York, inda sukayi kira ga kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya da ya goyi bayan aikawa da sojoji zuwa kasar Sudan ta Kudu domin kare rayukan ‘yan kasar.