Tace batu ne dake bukatar mayar da hankali akan sha'anin ilimimantar da miliyoyin matasa samari da 'yan mata ta hanyar basu ilimi irin na zamani tare da yin yaki da jahilci da kuma koyas dasu sana'o'in hannu.
Inji Irina, wajibi ne a saka kudaden da zasu cimma wannan burin na ilimantar da matasa da basu abubuwan yi. Tace hukumarta ashirye take domin tallafawa kasashe a wurin inganta lafiyar mata da yara kanana ta hanyar basu ilimin da zai anfanesu da jama'a..
Furucin na Irina Bokova dake ziyara a kasar ta Nijar tamkar albishir ne a ganin Hajiya Halima Sarmai ta kungiyar kare hakkin yara da mata. Tace furucinta su ne zai anfana ba wani ba. Tace su suna bude makarantun yaki da jahici a kowane gari suka je.
Ministan harkokin wajen Nijar Alhaji Ibrahim Yakuba yace baicin ilimin yara mata da mata gwamnatin Nijar na bukatar UNESCO ta ba 'yan jarida ilimi domin taimaka masu kara sanin makamar aiki.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani