Kungiyar masu yin brodi a Najeriya, shiyar arewa maso gabas, ta bada sanarwar cewa bata amince da wani sabon tsari ba da aka bukace ta da ta dinga biyan wasu kudaden aiyukan da ake gudanar mata zuwa cikin asusun wani kamfani mai zaman kansa a maimakon asusun hukumar NAFDAC.
Muhammadu Gidado Sani, shugaban kungiyar masu gasa brodi, na shiyar arewa maso gabas, yace makasudin gudanar da wannan taro shine domin su nuna rashin amincewarsu da wannan sabon tsari, yana mai cewar su ta bangarensu ci gaba da aiki da jami’an NAFDAC, shi yafi .
Ya ci gaba da cewa “idan har zasu biya kudi sun fi amincewa da su biya cikin asusun NAFDAC, domin mun tabbatar cewa idan kudaden suka shiga asusun NAFDAC, to lalle sun shiga asusun da zasu taimakawa Gwamnatin tarayya.”
Babban jami’in, hukumar NAFDAC, a jihar Bauchi, Mr. Stephen Layiko, ya shawarci masu gidajen brodi, dasu kai kukansu zuwa Abuja.