Kudirin ya bada izinin wa’adin shekara daya na dakarun da zai kunshi sojoji 11,200 da kuma yan sandan kasa da kasa 1,440.
Ana kyautata cewa dakarun MDD zasu maye gurbin dakaru 6,000 da kungiyar Afirika ke jagoranta yanzu a Mali. Zasu yi musaya daya ga watan Juli na wannan shekarar kodayake ana iya sake ranar. Yawancin dakarun Afirikan zasu zama dakarun MDD.
Kasar Mali ta fada cikin rikici bara yayinda sojoji suka hambare gwamnatin lamarin da yaba kabilar Abzinawa da mayaka masu alaka da kungiyar al-Qaida su kwace arewacin kasar. Dakarun Faransa da na Afirika sun taimaka wurin fatartakar yan yakin Islama daga yawancin biranen kasar amma an cigaba da samun hare-hare.