Mai magana da yawun rundunar, Janaral Chris Olukolade, yace an kashe sojoji uku a cikin gumurzun. Rikicin ya kara tsamari makon da ya wuce a sanadin abinda rundunar ta bayyana a zaman farmaki mafi girma da ta taba kaddamarwa a kan 'yan bindigar tun lokacin da suka fara tayar da kayar baya a shekarar 2009.
Mai magana da yawun rundunar bai bayyana inda fadan ya auku ba amma yace dakarun gwamnati na fafatawa cikin kwanaki biyun da suka gabata da mayakan Islama wadanda suka mallaki mugayen makamai.
Boko Haram, wadda ta ke kokarin kafa daular Islama a arewacin Najeriya, ta kai hare-haren bama-bamai da harbe-harbe a arewa, ciki har da munanan hare-hare a kan wasu garuruwa biyu cikin makonni takwas da suka gabata. Jami’ai sun ce mutane dari biyu da hamsin aka kashe a hare-haren da a ka kai kan garuruwan Baga da Bama.
A halin da ake ciki, an rufe bakin iyakar Najeriya da Kamaru, bayan da kasashen biyu suka cimma daidaito kan yadda za a tabbatar da nasarar matakan da aka dauka na damke 'yan bindigar da zasu yi kokarin sulalewa.
Wakilin sashen Hausa, Ibrahim Abdulaziz, ya aiko da karin bayani kan wannan daga Yola, hedkwatar Jihar Adamawa.