Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'ar Tarayyar Jos Ta Kaddamar Da Katamfaren Sashen Kulawa Da Cututtuka Marasa Yaduwa


Likitoci da maikatan asibiti suna duban mai ciwo
Likitoci da maikatan asibiti suna duban mai ciwo

Jami'ar tarayya dake Jos a jihar Filato ta kaddamar da katafaren sashe da zai kula da cututtukan koda, mafitsara, mahaifa da sauran cututtuka marasa yaduwa.

Cibiyar dake asibitin koyarwa ta jami'ar Jos da aka gina kan kudi kimanin naira biliyan daya, zata taimaka wajen rage tafiya kasashen ketare don neman jinya.

Shugaban jami'ar Jos, farfesa Tanko Ishaya wanda ya bayyana hakan, yayin da yake gabatar da ayyukan da yayi a shekaru biyu na kasancewarsa shugaban jami'ar ta Jos, ya kuma yabawa gwamnatin tarayya ta hannun gidauniyar tallafin ilimi a manyan cibiyoyin karatu a Najeriya, wato TET Fund kan yunkurin samarda na'urorin zamani don habaka bangaren kiwon lafiya a kasar.

Shugaban na jami'ar Jos, farfesa Tanko Ishaya ya kuma zayyana wassu ayyukan da ya gudanar a cikin shekaru biyu yana shugabancin jami'ar da suka hada da gine-gine, gyara dakunan kwanan dalibai da samun tallafin bincike daga gidauniyar Abdulsamad Rabiu, na naira miliyan dari biyu da hamsin, da sauransu.

Yayinda jami'ar ke murnar samar da cibiyar jinyar, a bangare guda kuwa bayanai na nuna yadda shugabannan likitoci a jihohi da dama na Najeriya ke kokawa kan janyewar likitoci daga asibitocin gwamnati, zuwa kasahen ketare don samun sukunin gudanar da ayyukansu da na'urori na zamani da gujewa yawan yajin aiki da kuma samun albashi mai tsoka.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG