A halin da ake ciki a yanzu ana fargabar mutum 11,587 sun kamu da cutar ta mashako yayin da aka tabbatar da mutane 7,202 a kananan hukumomi 105 daga jihohi 18 da ke fadin kasar sun kamu da cutar, inda cutar ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 453 a Najeriya.
Kashi 73 cikin dari na wadanda suka kamu da cutar yara ne daga shekara 1 zuwa 14.
Jihar Kano na daga cikin jihohin da cutar ta fi kamari, sauran jihohin sun hada da Yobe, Katsina, Borno, Kaduna, Jigawa, Bauchi, Legas, FCT, Gombe, Osun, Sokoto, Niger, Cross River, Enugu, Imo, Nasarawa da jihar Zamfara.
Daraktan tsare-tsare bincike da kidiggiga na hukumar lafiya matakin farko a Abuja Dr Abdullahi Bulama Garba yace hukumar su da sauran masu ruwa da tsaki abangaren lafiya sun dauki dukkan matakan dakile yaduwar ta inda tuni aka fara bada rigakafin cutar a wasu jihohi.
A nasa bangaren Dr. Lawal Musa Tahir, na Asibitin Nizamiye a Abuja ya ce cutar mashako na farawa da mura da zazzabi ya kuma jaddada hatsarin cutar tare da bada shawara don daukar matakan kariya.
Hakan dai ya biyo bayan yaki da Najeriya keyi ne da cututtuka kamar zazzabin cizon sauro, Zazzabin Lassa, da kuma cholera.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna