NIAMEY, NIGER - Rashin sanin takamammen dalilin zuwan ‘dan sandan a harabar jami’ar sanye da farin kaya da kuma yadda ya arce da gudu lokacin da Jandarmomi suka bukaci ya tsaya, ya sa suka bude masa wuta lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa a take, kamar yadda Sakataren kungiyar daliban jami’ar Abdoul Moumouni Dofo a Yamai Almoustapha Bakin Batoure ya shaidawa Muryar Amurka ta waya.
A cewar wasu bayanai ‘dan sandan mai suna Issa Ibrahim ya tafi jami’ar ne domin tattaunawa akan wata magana da daya daga cikin shugabaninta suka bukace shi, to amma rashin jittuwar da aka samu a tsakaninsa da wasu ‘dalibai ya sa suka bukaci dauki daga jami'an tsaron Jandarma da ke aikin tsaro a kewayen jami’ar.
‘Daliban na zargin yiyuwar wannan ‘dan sandan dan ta’adda ne da ya ke kokarin shiga jami’ar domin tafka ta’asa.
Lokacin da ya ga Jandarmomi sun iso sai ya fita da gudu lamarin da ya sa suka harba bindiga a sama a matsayin kashedi amma bai tsaya ba, dalili kenan suka bindige shi har lahira.
Kawo yanzu hukumomi ba su yi bayani game da wannan al’amari ba.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna