Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawagar Hukumar Kare Hakkin Dan Adam Ta Burkina Faso Ta Kai Ziyara Nijar


Bazoum Mohamed
Bazoum Mohamed

Tawagar jami’an hukumar kare hakkin dan adam ta kasar Burkina Faso, ta kai ziyara Nijar da nufin karawa juna sani sakamakon abinda aka kira jajircewar hukumar kare hakkin dan adam ta Nijar wato CNDH wajen fito da sahihan bayanan cin zarafi da toye hakkin jama’ar kasar ba tare da nuna son rai.

Mayar da hankali akan ayyukan kare hakkin dan adam ba sani ba sabo tare da mutunta ka’idodin aiki, ya sa hukumar CNDH shan yabo daga ciki da wajen kasar a tsawon shekaru 8 na shugabancin Pr. Khalid Ikrit.

Abinda kenan da ya sa a 2020 Majalisar Dinkin Duniya, ta saka ta a sahun hukumomi mafi kima da daraja a duniya akan batun kare hakkin dan adam wato "statut A."

Kwadayin samun irin wannan matsayi ya sa takwararta ta Burkina Faso aiko da tawaga da nufin daukan darasi.

Mme Antoinette Pouya Sawadogo ita ta jagoranci wannan tawaga takuma ce sun je ne don samun masaniya a game da hanyoyin da CNDH ke bi wajen tattaro bayanai a yayin ayyukan binciken tantance abubuwan dake nuni an take hakkin dan adam.

"Muna so (Nijar) ta bamu sirrin da ya bata damar haye stanin statut A." In ji Sawadogo.

Wahalhalun da matsalar tsaro ta jefa jama’ar Nijar a ‘yan shekarun nan inda ake zarin ‘yan bindiga da jami’an tsaro kowane a na sa bangare da laifin kuntatawa talakkawa, na daga cikin batutuwan da hukumar CNDH ta yi tsaye akansu don zakulo gaskiya lamari.

Yanayin da ake ciki a yau a Burkina Faso yana kama da wanda ake ciki a wasu yankunan Nijar.

Mme Antoinette Pouya ta ce ‘yancin rayuwa da ‘yancin samun tsaro da kare al’uma da dukiyoyi da ‘yancin zama a inda mutun ke so sun shiga cikin mawuyacin hali daga farkon wannan shekara kawo yau, ko da yake, gwamnati na iya kokarinta, amma abin na bukatar dubawa.

Hukumar CNDH ta Nijar ta yi farin cikin zuwan wannan tawaga domin a cewar wani kwamishininta Sani Korao abin alfahari ne a gare su da zai kara masu kwarin guiwar ci gaba da aiki ba tare da watajan kafa ba.

Hukumar kare hakkin dan adam ta CNDH wacce kundin tsarin mulkin kasa ya baiwa cikakken hurumi na kunshe ne da wakilan kungiyoyin kare hakkin dan adam na masanan doka irinsu lauyoyi da alkalai na abinda ke ba ta cikakken ‘yancin gudanar da aiki ba tare da samin umurni daga kowane bangare na hukuma ba.

A kasrhen makon nan ne jami’an ta ke kammala wa’adinsu na 2 na karshe.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Tawagar Hukumar Kare Hakkin Dan Adam Ta Burkina Faso Ta Kai Ziyara Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00


TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG