Rahotanni daga Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Sarkin masarautar Bungudu Alhaji Hassan Attahiru.
Masarautar Bungudu na jihar Zamfara ne a arewa maso yammacin Najeriya.
Bayanai sun yi nuni da cewa ‘yan bindigar sun sace basaraken ne da yammacin ranar Talata akan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Kafofin yada labaran Najeriya da dama sun ruwaito cewa ‘yan bindigar sun budewa ayarin motocin Sarkin wuta, inda su ma masu tsaron lafiyar basaraken su suka mayar da martani.
Sai dai maharan a cewar rahotanni, sun fi karfin jami’an tsaron da ke tare da Sarki Attahiru, lamarin da ya ba su damar sace shi.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa da misalin karfe 3:10 na yamma aka yi garkuwa da sarkin mai daraja ta daya, a wani yanki da ba shi da nisa da garin Kaduna.
Akalla dan sanda daya ya mutu a musayar wutar da aka yi tsakanin maharan da jami’an tsaro a cewar jaridar yanar gizo ta Dateline Nigeria.
Sace basaraken na kuwa ne kwana guda bayan da 'yan bindiga suka sako daliban makarantar Kaya a jihar ta Zamfara.
Kazalika lamarin ya faru ne 'yan kwanaki bayan da gwamna Bello Matawalle na Zamfara ya ce, gwamnatinsa ta rufe kofar yin afuwa da 'yan bindiga.