Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Muka Rufe Kofar Yin Afuwa Ga 'Yan bindiga – Matawalle


Gwamna Bello Matawalle (Facebook/Bello Matawalle)
Gwamna Bello Matawalle (Facebook/Bello Matawalle)

A makon da ya gabata aka katse hanyoyin sadarwa a Zamfara a wani mataki na shawo kan matsalar rashin tsaro da ta addabi jihar.

Gwamnan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya Bello Matawalle, ya ce dalilin daukar matakin rufe kofar yin afuwa ga ‘yan fashin daji shi ne, 'yan bindigar ba su yi amfani da damar da aka ba su ba a baya ba.

Matawalle ya bayyana hakan ne a karshen mako a Gusau, babban birnin jihar, inda rahotanni suka ambato shi yana cewa, a maimakon afuwa, dakarun kasar za su kawar da su ne.

“Gwamnati ba za ta kara mika shirin yin afuwa ga ‘yan bindiga ba, tun da sun ki su yi amfani da damar da aka ba su a baya.” Matawalle ya ce kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan ya ce 'yan bindigar sun nemi a yi zaman sulhu tsakaninsu da gwamnati.

Bayanai sun yi nuni da cewa, a ‘yan kwanakin nan dakarun Najeriya sun rutsa ‘yan fashin dajin da hare-hare, lamarin da yake sanadiyyar mutuwar da dama daga cikinsu, yayin da wasu ke tserewa zuwa jihohi da ke makwabtaka da Zamfara.

A makon da ya gabata aka katse hanyoyin sadarwa a jihar ta Zamfara lamarin da ya gurgunta harkokin kasuwanci, matakin da aka dauki makamancinsa awasu sassan jihar Katsina da ita ma ke fama da ‘yan fashin dajin.

Wasu gwamnonin jihohin arewa maso yammacin Najeriya sun sha gayyatar da ‘yan bindigar da su hau teburin tattaunawa, matakin da yake dorewa na dan kankanin lokaci.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG