Wasu mazauna yankin karamar hukumar mulki ta Dange Shuni da ke jihar Sokoto, wadda ke makwabtaka da jihar Zamfara, sun shaidawa Muryar Amurka cewa suna ganin ‘yan bindigar da yawansu suna ficewa daga jihar Zamfara ta wannan barin.
Wasu shaidun gani da ido sun ce mafi akasarin ‘yan bindigar a firgice suke, yayin da kuma akan hanyar su suke bin gidaje da shaguna suna kwacen abincin da za su ci.
Haka kuma an ruwaito cewa wasunsu kan tare ababen hawa su juye man fetur domin sakawa baburansu.
To sai dai duk da haka akwai rahotannin cewa wasu ‘yan bindigar da suka gudo, sun sace mutane kusan 20 a kauyukan Bissalam, Illelar Bissalam da Fajaldu, wadanda duk suke kan babban titin Sokoto zuwa Gusau, a cikin karamar hukumar mulkin ta Dange Shuni, ko da yake an ce wasu daga cikin mutanen da aka sace sun sami kubuta.
Kwamishinan lamurran tsaro na jihar Sokoto, Kanal Garba Moyi Isa mai murabus, ya tabbatar da haka a wata zantawa da Muryar Amurka ta wayar tarho, to amma kuma ya ce gwamnatin jihar ta dauki matakan hana ‘yan bindigar kwararowa a cikin jihar.
“Kananan hukumomin mulki 10 na jihar Sokoto da ke makwabtaka da jihohin Katsina, Zamfara da Kebbi, da kuma kasar Jamhuriyar Nijar, duk mun datse su, ba shiga ba fita daga jihar” in ji Kanal Moyi.
Dangane da aikin fatattakar ‘yan bindiga da sojoji ke yi a jihar Zamfara kuwa, Kwamishinan wanda tsohon jami’in soji ne, kuma masani lamurran tsaro, ya ce matakin yana tasiri sosai, to amma kuma akwai kura-kurai wajen daukar matakin.
Ya ce “Kamata ya yi a dauki mataki na bai daya a dukkan jihohin Zamfara, Katsina, Kebbi, Kaduna da Naija, ta yadda za’a sami murkushe ‘yan ta’addar a lokaci daya, ba tare da ba su damar tserewa zuwa wasu wurare ba.
Shi ma dai masani zamantakewa da halayyar dan adam, kuma shehin malami a jami’ar tarayya ta Birnin Kebbi, Farfesa Tukur Muhammad Baba, cewa yayi duk da yake matakan rufe kasuwanni da tituna da kuma Kafofin sadarwa sun jefa jama’ar jihohin cikin wani mawuyacin hali, to amma kwalliya ta soma biyan kudin sabulu, domin kuwa matakan sun kuma saka ‘yan bindiga cikin ukuba.
Ko Kun San Irin Makaman Da Sojoji Ke Amfani Da Su Wajen Yaki Da 'Yan Bindiga A Jihar Zamfara?
To sai dai shi ma ya yaba da tasirin matakin da gwamnatin tarayya take dauka na kai farmaki a jihar ta Zamfara, wanda a cewarsa, tun tuni ya kamata a dauki irin wannan matakin.
Amma kuma ya shawarci gwamnati da ta dauki irin wannan matakin lokaci daya a dukkan jihohin Arewa maso yamma da ke fuskantar kalubalen tsaro.
Rahotanni dai na nuna cewa dakarun sojin Najeriya na ci gaba da luguden wuta ta sama da kasa kan sansanonin ‘yan bindiga a jihar Zamfara, kari ga dokokin gwamnatin jihar na rurrufe kasuwanni, tashoshin mota da haramta sayar da man fetur a jarka, wadanda suka taru suka jefa ‘yan bindigar cikin rudu da tashin hankali.
Saurari tattaunawa da Kanal Garba Moyi Isa, Kwamishinan lamurran tsaro a jihar Sokoto: