Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar Dake Mulki a Nigeria Tayi Watsi da Cewa Rahotannin Barkewar Rikici ka Iya Janyowa Jam'iyyar Cikas a Zaben 2015


Shugaba Goodluck Jonathan
Shugaba Goodluck Jonathan

Jam'iyyar PDP dake mulkin Nigeria tayi watsi da rahotannin da ake yayatawa cewar rahotannin chanjin sheka ka iya janyowa jam'iyyar cikas a babban zaben da za'a yi a shekarar 2015.

Mai Magana da yawun jam'iyyar PDP dake mulkin Nigeria, yayi watsi da rahotannin da ake yayatawa cewar ficewar da wasu gwamnonin jihohi suka yi daga cikin jam'iyyar zuwa jam'iyyar hamayya ta (APC), hakan na neman janyowa jam'iyyar cikas dab da yunkurowar da babban zaben shugaban kasa a shekarar 2015.

Anji daga bakin Abdullahi Jalo na fadin cewa ficewar da wasu muhimman Gwamnonin suka yi daga jam'iyyar zai ma kara mata kwarjini ne da farin jini, kuma hakan ya nuna irin yadda jam'iyyar ke kara karfi a tsarin salon mulkin Dimokuradiyya.

Gwamnonin jihohin dake karkashin inuwar jam'iyyar PDP yanzu suka bada sanarwar ficewa sun kafa reshe mai karfin da suka sanyawa sunan sabuwar jam'iyyar PDP,wato (NPDP) a wani babban taron da suka gudanar, wanda aka tashi baram-baram. Daga cikin Gwamnonin jihohin da suka yada kwallon Mangwaro domin hutawa da kuda, sun hada ada Rotimi Amaechi na jihar Rivers, da Rabi'u Musa Kwankwaso na jihar kano, da Aliyu Wamakko na jihar Sakkwato, da Sule Lamido na jihar Jigawa da Murtala Nyako na jihar Adamawa.

Masu fashin bakin al'amuran yau da kullun sun yi hassashen cewar chanjin shekar da Gwamnonin suka yi daga jam'iyyar ta PDP ka iya janyowa kokarin da shugaba Goodluck Jonathan keyi na sake neman yin takara. Ya zuwa yanzu dai Mr. Jonathan bai ayyana cewar zai sake neman yin takarar matsayin shugaban kasa ba, amma kuma Jalo yaki cewa komai game da ko Jonathan nada alamar samun nasara a zaben shugaban kasa mai zuwa.
XS
SM
MD
LG