Gwamnonin sun hada da na Jihar kano, da jihar Sokoto, da jihar Adamawa, da jihar Rivers, da kuma jihar Kwara da Talata suka bayyana cewar sun yi kaura zuwa jam'iyyar "All Progressives Congress, ko APC a takaice."
Rahotannin farkon da aka samun sun bayyana cewa Gwamnonin jihohin Niger da Jigawa, suma suna kokarin bin sahun 'yanuwansu, amma gwamnoni biyun sun musanta haka.
An dai riga an san irin yadda Gwamnonin jihohi keda karfin fada aji a Nigeria, kuma ficewa daga cikin jam'iyyar dake mulki zuwa jam'iyyar hamayya ta APC da Gwamnoni biyar suka yi, haka zai karfafa gwiwar jam'iyyar hamayya ta APC a Majalisaar dokoki. Kazalika, hakan ya baiwa jam'iyyar ta APC cikakkiyar dama da karfin kalubalantar shugaba Goodluck Jonathan da jam'iyyar PDP a babban zaben shugaban kasa da sauran zabuka a shekarar 2015.
Shekaru goma sha biyar ke nan da jam'iyyar PDP tayi tana rike da ragamar mulkin Nigeria, amma duk da haka tana fama da rigingimun cikin gida, musamman ma cece-kucen da aka rika yi tun kammala zaben shugaba Jonathan a shekarar 2011.
Da yawa daga cikin 'yan Arewa na cewa Jonathan, wanda Kirista ne daga yankin kudancin Nigeria, yaki yin aiki da dokokin da aka gitta wadanda ba a rubuce suke ba dake neman sai lallai a rika karba-karba a zaben shugaban kasa, a tsakanin yankin kudanci da mabiya addinin Kirista keda rinjaye da kuma yankin Arewa da Musulmi keda rinjaye.
Jonathan ya sami nasarar hawa kujerar shugaban kasa ne bayan rasuwar marigayi Umaru Yar'Adua wanda Musulmi ne a zagayen farko na shugabancinsa. A watan Agustan da ya gabata ne gwamnonin jihohin da yanzu ke kaura suka fice daga jam'iyyar PDP. Sun kuma hada daga bangarorin Musulmin Arewa da Kiristocin Kudancin Nigeria.