Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Burtaniya Ta Tashi Tsaye Domin Yakar Ta'addanci


Firai ministar Burtaniya, Theresa May
Firai ministar Burtaniya, Theresa May

Wani harin da jami'an tsaro suka ayyana a matsayin na ta'addanci ne da aka kai a Burtaniya, ya sa hukumomin kasar sun tashi tsaye wajen tunkarar kalubalen hare-haren ta'addancin.

Burtaniya ta kara tsaurara matakan kariya daga hare-haren ta’addanci, bayan wani harin bam da aka kai a tashar jirgin kasa, wanda kungiyar IS ta dauki alhakin kai wa.

A jiya Juma’a, Firai Minista Theresa May, ta bayyana daukan wannan mataki, wanda Cibiyar nan ta hadin gwiwa mai bin diddigin hare-haren ta’addanci, ta ba da shawarar a yi – inda aka kai baranzar harin ta’addanci zuwa ma’auni na karshe.

Firai ministar ta kara da cewa, dakarun kasar za su fara taimakawa ‘yan sanda wajen ba da tsaro a wasu wurare, tana mai cewa al’umar kasar za su ga karin jami’an tsaro akan tituna, ba kamar yadda aka saba gani a baya ba.

Yayin da hakan ke faruwa, kungiyar IS, ta ce wani reshenta ne ya dana bam din da aka tayar a tashar Parsons Green Subway, wanda ya raunata mutane 29.

Bam din ya tashi ne, a daidai lokacin da ake samun cunkoson jama’a, a harin wanda ‘yan sanda suka ayyana shi a matsayin na ta’addanci.

Daga cikin wadanda suka jikkata, babu wanda rayuwarsa ke cikin hadari, in ji ma’aikatan ba da agajin gaggawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG