Hedikwatar Tsaron Amurka ta Pentagon ta ce Koriya Ta Arewa ta sake harba wani makami mai linzami mai matsakaicin zango da asubahin yau dinnan Jumma'a. Makamin ya bi ta kan tsibirin Hokkaido, mallakin Japan, kafin ya fada cikin tekun Pacific.
Nan da nan kasar Japan ta yi amfani da kakkausan harshe wajen nuna bacin ranta ga Koriya Ta Arewa saboda harba wannan makamin. Babban jami'in da ke magana a madadin kasar ta Japan ya ce, "Japan ba fa za ta lamunta da takalar da Koriya Ta Arewa ta ke yi akai akai ba."
Wannan harba makamin ya zo ne 'yan kwanaki kawai bayan da Kwamitin Sulhun MDD ya kakaba takunkumi mafi tsanani ga Koriya Ta Arewar saboda shirinta na nukiliya da kuma kin daina gwaje-gwajen makamai masu linzami da ta ke yi. Kafar labarai ta Reuters ta bayar da rahoton cewa Kwamitin Sulhun MDD, zai yi zama a yau dinnan Jumma'a da karfe 3 na yamma kan harba makami na baya bayan nan da Koriya Ta Arewa ta yi.
Duk da gargadi da kuma matakin ladabtarwa da aka dauka kan Koriya Ta Arewa ta cigaba da gwaje-gwajen makamai
WASHINGTON D.C. —
Facebook Forum