Karshenta dai babban sakataren MDD Antonio Guterres ya fito karara yana cewa abinda hukumomin kasar Myanmar ke wa dubban dubatan mutanen jinsin Rohingya, wani mataki ne na kawar da su daga doron kasa da kuma raba kasar da su baki daya.
Da yake amsa tambayar dalilin da yassa ya yanke wannan wannan hukuncin gameda lamarin da ke shahuwar ‘yan Rohingya din, wadanda aksarins Musulmi ne, Sakataren yace, “idan kayi wani abu da zai tilastawa sulusi daya na daukacin mutanen Rohingya dake a kasa su tashi, ba shiri, su barta, me zaka kira wannan al’amari?”
Saboda haka ne Magatakardan na MDD, a kalamin da yayi a hedkwatar Majalisar dake birnin New York, ya nemi hukumomin na kasar Myanmar da su dakatarda matakan sojan da suke dauka, a kawo karshen wannan tashin hankali kuma a bar doka tayi aikinta, a kuma tabattarda ganin cewa duk mutanen da aka tilastawa barin kasar, an kyale su sun dawo kasarsu.
Sai dai har yanzu hukumomin kasar ta Burma suna ci gaba da nacewa akan cewa duk wannan tashin hankalin ya samo asali ne daga ran 25 ga watan Agustan da ya wuce, lokacinda wani gungun ‘yanatwayen Rohingya suka abkawa wasu ma’aikatun ‘yansanda, don maida martini akan kuntatatwar da ake da ake musu.
Mutane kamar 400 aka hallaka a cikin hare-haren ramuwar gayyar da ma’aikatan tsaro suka maida akan ‘yan Rohingya din.
Facebook Forum