Daga daurin talala, hukumomin kasar jamahuriyar Nijer sun maida tsohon shugaban kasar Mamadou Tandja gidan kaso bisa tuhumar shi da laifin azurta kai da dukiyar kasa.
Jami’an gwamnatin kasar jamahuriyar Nijer sun ce umarnin kotu su ka bi, a jiya lahadi su ka mika Mr.Tandja ga gidan kason Kollo, wanda ke kusa da Niamey babban birnin kasar.
Mr.Tandja ne ya yi mulkin kasar jamahuriyar Nijer daga shekarar 1999 har ya zuwa lokacin da sojoji su ka hambare shi a shekarar da ta gabata da ya yi kokarin yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima don ya tsawaita wa’adin shi na mulki.
Gwamnatin mulkin sojin kasar ta zargi Mr.Tandja da wawashe baitalmalin da ya kai kimanin dola miliyan 125 a lokacin mulkin shi.
Kasar jamahuriyar Nijer babbar mai saidawa kasashen waje ma’adinin uranium ce. Shugaban kasar na yanzu, janar Salou Djibo ya yi alkawarin maida kasar ga mulkin farar hula. Kuma za a yi zaben shugaban kasa zagayen farko a ranar 31 ga watan nan na janairu.