Kasar Italiya ta kasance kasa ta uku da ta bayyana amincewa da majalisar wucin gadi ta ‘yan tawaye a matsayin halaltacciyar gwamnati a kasar Libya dake arewacin nahiyar Afrika. Wani mataki da ya gurguntar da yunkurin da gwamnatin Moammar Gadhafi da kuma ‘ya’yansa biyu ke yi na sasantawa ta hanyar diplomasiya.
Ministan harkokin kasashen ketare na Italiya, Franco Frettini, ya bayyana jiya Litinin a birnin Rome cewa, kasar ta tsaida shawarar amincewa da Majalisar Wucin Gadi a matsayin halaltacciyar wakiliyar mutanen kasar Libya ita kadai. Bisa ga cewarsa, Italiya zata aika da manzo zuwa birnin Benghazi inda gwamnatin ‘yan tawayen take, cikin ‘yan kwanaki kalilan.
Italiya ta bi sahun Faransa da Qatar wajen amincewa da majalisar ‘yan tawayen. Frattini ya kuma marabci manzon ‘yan tawayen ali al-Essawi, wanda yace ba za a amince da maye gurbin Mr. Gahdafi da dansa ba.
Jaridar The New York Times ta buga labarin cewa, a kalla ‘ya’yan shugaban kasar Libya guda biyu sun yi tayin cewa, Mr. Gahdafi ya mika mulki ga gwamnatin rikon kwarya ta damokaradiya karkashin jagorancin danshi, Seif al-Islam Gadhafi. Sai dai kakakin gwamnatin Mussa Ibrahim ya bayyana jiya Litinin cewa, yayinda Libya take a shirye domin shawo kan rudamin ta hanyar diplomasiya, tare da hadin guiwar manyan kasashen duniya, gwamnati ba zata yi wata shawara a kan makomar Mr, Gadhafi ba.
Bisa ga cewarshi, za a iya gudanar da zabe, ko kuri’ar raba gardama, ko wani abu dabam, amma tilas ne Mr. Gadhafi ya jagoranci duk wani tsarin mika mulki.
Tashar talabijin ta kasar ta nuna Mr. Gadhafi na dan karamin lokaci yana dagawa magoya bayanshi hannu a kofar gidanshi dake Tripoli. Wannan ce fitar Mr. Gadhafi ta farko a bainin jama’a cikin sama da mako guda.