Gungun mayakan ‘yan tawayen na Libya sun fita ne daga cikin tankunan yakin da suke ciki suna daga hannu domin neman agajin jiragen saman NATO das u kai masu dauki lokacin da suke kokarin kora mayakan Gadhafi zuwa baya. Har yanzu dai ba’a tantance ko jirgin saman yakin na NATO da yayi harbin daga sama yayi ne cikin ganganci ko kuskure ne ya faru amma jami’an NATO sun ce tuni har sun fara gudanar da bincike. Kafofin labarun Yammacin Turai sun yayata rahoton cewa Asibitin da ake kula dawadanda suka jikkata dake Ajdabiyah ya cika makil da majiyatta. A kwanakin baya ne dama shugabannin mayakan ‘yan tawayen Libya suka yizargin cewa jiragen saman yakin NATO na yawaita kaiwa mayakan ‘yan tawayen hare-hare maimakon maida hankali wajen kare farar hular Libya.
Hare-haren jiragen saman yakin da rundunar tsaron turai ta NATO ke kaiwa a sararin samaniyar kasar Libya sun halaka mayakan ‘yan tawayen Libya biyu a kusa da yankin gabashin Brega, wasu kuma da yawa sun jikkata. NATO na kai hare-haren ne domin kare farar hula daga kuncin Gwamnatin shugaba Moammar Gadhafi.