Kasashen NATO sun yarda zasu karbi ragamar jagorancin aikin hana jiragen saman yaki shawagi a samaniyar Libya, su na kuma nazarin ko zasu rungumi wasu ayyukan na gudanar da dukkan ayyukan soja a kasar dake Afirka ta Arewa. Jiya alhamis, babban sakataren NATO, Anders Fogh Rasmussen, yace nan da kwana uku kungiyar kawancen tsaron zata fara karbar ragamar aikin hana jiragen yaki shawagi a samaniyar Libya. Rasmussen yace za a gudanar da wannan aikin ayyin da ake gudanar da aiki mafi wuya da sarkakiya na hare-haren bam da sojojin taron dangi ke kaiwa a kan sojojin kasa na Libya. Jagoran na NATO yace a yanzu dai, NATO ce zata rika gudanar da aikin hana shawagin jirage a yayin da kasashen da suka yi kawancen taron dangi kan Libya zasu gudanar da nasu aikin na kai hare-haren bam. Yace watakila nan da kwanaki biyu za a iya cimma daidaituwa a kan mika dukkan ayyukan a hannun NATO. Turkiyya, kasar Musulmi kwaya daya tak dake cikin NATO, ta yarda da wannan shirin jiya alhamis a bayan tattaunawar da aka yi lokaci guda ta wayar tarho a tsakanin sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton da takwarorinta na Turkiyya da faransa da Britaniya. Turkiyya ta nemi a ba ta tabbacin cewa ayyukan da NATO zata gudanar takaitattu ne, kuma za a dauki matakan hana yiwuwar kashe fararen hula Musulmi. Har ila yau a jiya alhamis, Amurka da Faransa sun ce hadaddiyar daular Larabawa zata bayar da gudumawar jiragen sama 12 da zasu rika shawagin tabbatar da yin aiki da haramta shawagin jiragen sama a Libya, abinda ya sa ta zamo kasar larabawa ta biyu bayan Qatar da ta shiga wannan taron dangi. Ana sa ran nan da ‘yan kwanaki kadan jiragen saman Qatar zasu fara shawagi a samaniyar Libya. A jiya alhamisar kuma, sojojin taron dangi sun kai farmaki kan cibiyoyin sojan gwamnatin Libya. Jiragen yakin Faransa sun harbo wani jirgin yakin gwamnatin Libya a samaniyar birnin Misrata. Har ila yau, sojojin faransa sun ce sun kai wani hari can cikin kasar ta Libya a kan wani sansanin mayakan sama dake wuri mai tazarar kilomita 250 a kudu da bakin gabar tekun bahar Rum. Amma duk da haka, sojoji masu yin biyayya ga Gaddafi sun ci gaba da kai farmaki a kan biranen Ajdabiya da Misrata a bakin gabar tekun.
Kungiyar NATO ta yarda zata karbi jagorancin hana shawagin jiragen sama a sararin samaniyar Libya.
Kasashen NATO sun yarda zasu karbi ragamar jagorancin aikin hana jiragen saman yaki shawagi a samaniyar Libya, su na kuma nazarin ko zasu rungumi wasu ayyukan na gudanar da dukkan ayyukan soja a kasar dake Afirka ta Arewa. Jiya alhamis, babban sakataren NATO, Anders Fogh Rasmussen, yace nan da kwana uku kungiyar kawancen tsaron zata fara karbar ragamar aikin hana jiragen yaki shawagi a samaniyar Libya.