Ministan harkokin wajen Libya Moussa Koussa yayi murabus bayan ya isa Ingila,inda ya bayyana cewa ya bar gwanatin Moammar Gadhafi.
Ma’aikatar harkokin wajen Ingila ta fada jiya laraba cewa Mr. Koussa ta kashin kansa yayi balaguro daga Tunisia zuwa Ingila,inda ya gayawa jami’an gwanatin kasar cewa yayi murabus.Daga nan jami’an gwmnatin Ingila suka shawarwaci sauran magoya bayan Gadhafi suma su dare wa masa.
Wani kakakin gwamnatin Libya Moussa Ibrahim, ya karyata cewa ministan harkokin wajen ya sake sheka,yana mai cewa yana Ingila ne domin harkokin difilomasiyya. A farko farkon rikicin kasar, ministan harkokin cikin gida,da na shari’a suma suka yi murabus suka hade da ‘yan tawaye da suka fara fada daga gabashin kasar.
Ahalin yanzu kuma Britaniya ta kori jami’an jakadancin biyar daga ofishin jakadancin Libya dake London domin suna muzgunawa ‘yan hamayya,da kuma barzana ga tsaron Ingila.
Sakataren harkokin wajen Ingila William Hague ne ya bayyana haka jiya laraba,yace jami’an da aka kora har da hafsan soja dake ofishin jakdancin.