Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka tayi watsi da kiran da Gadhafi ya yi na tsagaita harin sararin sama


Shugaban kasar Libya Moammar Gahdafi.
Shugaban kasar Libya Moammar Gahdafi.

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton, ta yi watsi da bukatar da Gaddafi ya nema da kansa, cewa a kawo karshen hare-haren da NATO ke kaiwa dakarunsa

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton, ta yi watsi da bukatar da Gaddafi ya nema da kansa, cewa a kawo karshen hare-haren da NATO ke kaiwa dakarunsa, ta ce ya kamata Gaddafi ya mika ragamar iko ya nemi mafaka a wata kasar. Clinton ta fadi jiya Laraba a birnin Washington cewa Gaddafi ya san tilas ne ya tafi. Ta jaddada cewa Amurka da NATO na bukatar magoya bayansa su koma baya su kuma daina kai hari. Fadar Shugaban Kasa ta White House ta tabbatar da samin wata wasikar kuma daga Gaddafi. Abinda ke kunshe cikin wannan birkicacciyar wasika mai shafuka uku, wadda aka raba wa manema labarai na nuna cewa Shugaban na Libiya ya nemi da Mr. Obama ya daina abin da ya kira, “yaki na rashin adalci a kan karamar kasa. ”A birnin Misrata na yammacin kasar da kuma Brega da ke gabashi, wadanda ke karkashin ikon ‘yan tawaye, dakarun da ke biyayya ga Gaddafi sun cigaba da barin wuta kan mayakan ‘yan tawaye da rokoki da atilari a jiya Laraba.

A wani koma baya ga ‘yan tawayen, hare-haren tsawon kwanaki uku da dakarun Gaddafi su ka yi ta kaiwa sun hana ayyuka a rijiyoyin mai da ke karkashin ikon ‘yan tawaye a gabashin kasar. Kakakin ‘yan tawayen Abdel-Hafidh Ghoga yace wani ayarin tankokin yaki da ke kuma tafe da atilare ya kai hari kan wuraren mai biyu a yankin hamadar da ke kudu.Ghoga ya fadi jiya Laraba cewa ‘yan tawayen sun mai da martani da tsaurara matakan tsaro, ciki har da zakudar da mayakan don kare wuraren mai din. Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Libiya, Khaled Kaim yace wani jirgin yakin Burtaniya ya kai hari kan manyan rijiyoyin man Sarir a jiya Laraba, ya hallaka wasu masu gadi uku. Da NATO da Burtaniya dai duk babu kowannensu da ya ce wani abu game da wannan zargin.

XS
SM
MD
LG