Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Yi Barazanar Kai Wa Iran Hari Kai Tsaye Idan Iran Ta Kai Hari Daga Yankinta


NETANYAHU
NETANYAHU

Ministan harkokin wajen Isra'ila ya yi barazana a yau Laraba cewa, sojojin kasarsa za su kai farmaki kan Iran kai tsaye idan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai hari daga yankinta kan Isra'ila.

WASHINGTON, D. C. - Kalaman nasa sun zo ne a daidai lokacin da ake kara samun takun saka tsakanin kasashen da ke gaba da juna bayan kisan Janar na Iran a wani harin da aka kai a karamin ofishin jakadancin Iran da ke Siriya a farkon watan nan.

"Idan Iran ta kai hari daga yankinta, Isra'ila za ta mayar da martani kuma ta kai hari a Iran," in ji Israel Katz a cikin wani sakon da aka buga akan X a cikin Farsi da Hebrew.

A safiyar yau Laraba, Jagoran Musulunci na Iran Ayatullah Ali Khamenei ya sake jaddada alkawarin mayar da martani ga Isra'ila kan harin da aka kai karamin ofishin jakadancinta da ke Damascus.

Tehran ta dora alhakin harin da Isra'ila ta kai kan ginin da ya kashe mutane 12. Isra'ila dai ba ta amince da hannunta a harin ba, ko da yake ta yi ta shirin yiwuwar mayar da martani da Iran ka iya yi.

Khamenei ya yi magana ne a wajen wani taron addu'o'i na murnar kawo karshen watan Ramadan mai alfarma, yana mai cewa harin da aka kai ta sama "ba daidai ba ne" kuma tamkar kaiwa kasar Iran hari ne.

"Lokacin da suka kai hari a ofishin jakadancinmu, kamar sun kai hari kan yankinmu ne," in ji Khamenei, a cikin jawabin da gidan talabijin na kasar Iran ya watsa. "Dole ne a hukunta muguwar gwamnati, kuma za a hukunta ta."

Katz ko Ayatullah ba su yi karin haske kan hanyar da za su mayar da martani ba.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG