Lamarin da ke kara ta’azzara a yakin da ake gwabzawa tsakanin Isra'ila da abokan gabanta a yankin, kuma Iran ta ce harin ya yi sanadin mutuwar mashawartan sojoji bakwai da suka hada da manyan kwamandoji uku.
Wakilan Reuters a wurin da ke gundumar Mezzeh da ke Damascus, sun ga ma'aikatan agajin gaggawa suna hawa kan baraguzan ginin da ya ruguje a cikin harabar jami'ar diflomasiyya na babban ginin ofishin jakadancin.
An hangi ministan harkokin wajen Syria da ministan cikin gida duka a wurin. Ministan harkokin wajen Syria Faisal Mekdad ya ce "muna Allah wadai da wannan mummunan harin ta'addanci da aka kai kan ginin karamin ofishin jakadancin Iran da ke Damascus tare da kashe wasu da ba su ji ba ba su gani ba."
Isra'ila dai ta dade tana kai hare-hare kan sansanonin sojin Iran da ke Syria da na 'yan kawayenta, sannan ta kara kai hare-hare a daidai lokacin da take kai farmaki kan kungiyar Hamas da ke samun goyon bayan Iran a Zirin Gaza.
Tun bayan harin Gaza da kungiyar Hamas ta kai a kudancin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, sojojin Isra'ila sun kara kai hare-hare ta sama a kasar Syria kan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran da kungiyar Hizbullah da ke samun goyon bayan Iran, wadanda dukkansu ke goyon bayan shugaban kasar Syria Bashar al-Assad.
Harin na ranar Litinin shi ne karo na farko da Isra'ila ta kai wani katafaren ginin ofishin jakadancin da kanta.
Dandalin Mu Tattauna