ABUJA, NIGERIA - Batun rikicin na Falasdinawa da Yahudawa na daga abin da ke dauke hankalin mutane a Najeriya cikin lamuran kasashen duniya.
Isra'ila da ke da huldar jakadanci da Najeriya na da wasu yarjeniyoyin tsaro da kasar, kuma duk shekara dubban mabiya addinin Kirista a Najeriya kan kai ziyara Urshalima a garuruwan Israila, yankin Falasdinawa, tuddan Golan da ma cikin Masar don addu'a a sassan tarihi da ke da nasaba da Yesu Almasihu.
A sharhinsa, Farfesa Sani Yahaya ya ce tura ce ta kai bango ya sa 'yan Hamas turjiya amma shiga tsanaki a yanzu shi ne mafi a'ala
“Wannan akasi kowa ya sani a duniya an dade a na yi, ga shi nan yanzu ya kawo mugun asarar rayuka. Majalisar Dinkin Duniya ta zauna ta yi adalci.”
Pastor Simon A. S sakataren kungiyar Kiristoci na jihohin Arewa ta tsakiya ya ziyarci Isra'ila sau da dama yana mai cewa fadan ya so ya wuce na harshe da hakori ne tsakanin 'yan uwa na tarihi.
"Na je na ga Musulmi, Kirista da Yahudawa na zaune tare kuma wani mabudin wajen ibadar mabiya addinin Kirista ma na hannun Musulmi ne."
Shi kuma shahararren shugaban kungiyar matasa ta Najaeriya Komred Murtala Garba ya bukaci matasan sassan biyu su yarda gora don duniyar yau ba ta zaman kiyayya ba ce.
Hakika akwai masu marawa Falasdinawa baya a Najeriya da kuma masu kaunar Isra’ila da yiwuwar ba wa kowane bangare uzuri a irin wannan yanayi na zubar da jini.
Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-Hikaya:
Dandalin Mu Tattauna