Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Falasdinawa Sun Amince Da Shawarar Amurka Kan Dakatar Da Gine-Gine


Shugaban Falasdinawa, Mahmoud Abbas
Shugaban Falasdinawa, Mahmoud Abbas

Wani babban mashawarcin Falasdinawan yace sun yarda da shawarar da Amurka ta gabatar ta dakatar da gine-gine na karin kwanaki 60 muddin za a iya cimma yarjejeniya kan iyakar Isra'ila da Falasdinu cikin wa'adin dakatartwar.

Wani babban jami’in shawarwarin Falasdinawa yace bangarensa ya amince da shawarar da Amurka ta gabatar ta dakatar da karin gine-ginen gidajen da Isra’ila take yi ma yahudawa a yankin yammacin kogin Jordan na wasu kwanaki 60, muddin dai za a iya cimma daidaituwa a kan iyakokin Isra’ila da kasar Falasdinu cikin wannan lokacin.

Nabil Shaath ya fada jiya alhamis cewa idan har ba a cimma yarjejeniya kan bakin iyakokin sassan biyu cikin watanni biyu ba, to tilas a kara wa’adin dakatar da gine-ginen.

Wannan furuci na Nabil Shaath yana zuwa a daidai lokacin da jakadan Isra’ila a Amurka, Michael Oren, yake gaskatawa a karon farko cewa Amurka ta gabatarwa da Isra’ila abinda ya kira wani irin tukuici domin gwamnatin kasar ta kara wa’adin dakatar da gine-ginen. Oren yace yana sa ran za a gabatarwa da Amurka amsar wannan tayin nan da sa’o’I 48.

Fadar White House dai ta musanta cewa shugaba Barack Obama ya aike da wasika ga firayim ministan bani Isra’ila, Benjamin Netanyahu, yana tayin tallafin soja da goyon bayan diflomasiyya da wasu abubuwan domin Isra’ila ta kara wa’adin dakatar da gine-ginen sau guda.

A yau jumma’a shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas zai gana da ministocin harkokin wajen kasashen larabawa a Libya, inda ake sa ran zai yanke shawarar ko zai tsinke tattaunawar neman zaman lafiyar da ake yi da Isra’ila.

XS
SM
MD
LG