Shugaban Amurka Barack Obama yace ba za a iya cimma burin wanzar da zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Palasdinuwa ta hanyar yanke ba, yayinda takwaranshi na kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya shawarta tsaida wa’adin shekara guda na warware rikicin.
Shugabannin biyu sun gabatar da jawabai jiya Laraba a zauren taron Majalisar Dinkin Duniya. Shugabannin Palasdinawa suna shirin gabatar da bukatar kasancewa kasa mai cin gashin kanta a gaban kwamitin sulhu na MDD gobe jumma’a.
Mr. Obama ya bayyana rashin gamsuwa da tafiyar hawainiyar da yunkurin wanzar da zaman lafiyan ke yi, sai dai ya hakikanta cewa, ta hanyar tattaunawa tsakanin Isra’ila da Palasdinawa ne kadai za a iya warware rikicin amma ba a zauren Majalisar Dinkin Duniya.
Mr. Sarkozy a nashi bangaren cewa yayi bayan shafe shekaru 60 ana kokarin wanzar da zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Palasdinu ba tare da cimma nasara ba, lokaci ya yi na sake dabara. Ya bada shawarar sake komawa teburin tattaunawa a cikin wata guda, da tsaida yarjejeniya dangane da kan iyaka cikin watanni shida, a kuma cimma matsaya cikin shekara daya.
Ya kuma shawarata daga matsayin gwamnatain Palasdinawa a Majalisar Dinkin Duniya daga mai sa ido, zuwa memba marar ikon fada aji, canjin dake bukatar samun karamin rinjaye idan aka kada kuri’a a Majalisar Dinkin Duniya mai membobin dari da casa;in da uku.
Jiya Laraba shugaba Obama ya gana da Firai Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu inda ya jadada himmar Amurka na tabbacin tsaron Isra’ila. Mr. Obama ya kuma tattauna a lokuta dabam dabam da shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya.