Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Haramta Wa Gwamnatin Tarayya Daukar Ma’aikata Daga Ketare


Shugaban Amurka Donald Trump a jiya Litinin ya sanya hannu a kan dokar da ta haramtawa ma’aikatun gwamnatin tarayya daukar ma’aikata daga kasashen waje su yi ayyukan da Amurka ke yi.

Fadar White House ta ce dokar umarnin shugaban kasar zata taimaka wurin haramtawa ma’aikatun gwamnati maye gurbin Amurkawa ma’aikata ba bisa ka’ida ba da ‘yan kasar waje don neman rahusa.

Dokar ta bukaci duk ma’aikatun gwamnati su kamala bincike su nuna ko suna daukar ‘yan asalin Amurka da ‘yan kasa aiki a kan mukaman aiki da mutane da dama ke nema.

Trump ya ce matakin da yake daukar ya biyo bayan wata sanarwa daga ma’aikatar Valley Authority ta jihar Tennessee cewa zata bada kashi 20 cikin dari na ayyukan fasaha ga kamfanonin dake kasashen waje, wanda zasu yi amfani da takardar biza ta H-iB.

Wannan dokar umarnin shugaban kasa na zuwa ne yayin da wasu ‘yan jaridar Muryar Amurka suke zaman jiran tsammani ko za a sabonta musu takardun bizar su ta J-1 bayan da ma’aikatar ta sake duban takardun bizar ma’aikata.

Trump ya fadawa manema labarai a jiya Litnin cewa zai kori shugaban ma’aikatar TVA mai suna Skip Thompson saboda yana daukar ‘yan kasar waje kuma yana daukar albashi mai yawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG