Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pompeo Ya Ce Ba Za A Kyale China Ta Ci Zarafin Masu Fafutuka Ba


Mike Pompeo
Mike Pompeo

A jiya Talata Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ya yi alkawarin ba da kariya ga masu rajin demokradiyya a Hong Kong wadanda suka tsere daga garin kuma suka la'anci China bayan da Beijing ta ce, an baiwa 'yan sanda umarnin kama masu fafutukar daga ƙasashen waje.

A cikin wata sanarwa da Pompeo ya fitar ya ce, "Jam'iyyar masu ra’ayin gurguzu ta China ba za ta iya amincewa da 'yantar da jama'arta ba, kuma tana kara kokarin fadada karfin ikonta zuwa wajen iyakokinta".

"Amurka da sauran kasashe masu 'yanci za su ci gaba da kare al’ummar mu daga dogon ikon mulkin mallakar Beijing.

A cikin wata sanarwar kuma a shafin twitter, Pompeo ya ce, Washington "ta yi Allah waddai da yunkurin jam'iyyar gurguzu ta China na muzgunawa 'yan rajin dimokiradiyya wadanda ke zaune a wajen China, ciki har da Amurka."

Kafafen yada labarai na kasar China sun fada a safiyar Juma'a da ta gabata cewa, 'yan sanda a Hong Kong sun ba da umarnin kama wasu masu fafutukar kare dimokuradiyya shida da ke zaman gudun hijira bisa zargin keta sabuwar dokar tsaro.

Daya daga cikin su, Samuel Chu, shugaban majalisar dimokradiyya ta Hong Kong da ke Washington, ya rubuta a shafin Twitter cewa ya kasance Ba’Amurka tsawon shekaru 25 kenan.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG