Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Daular Islama na Neman Yiwa 'yan kabilar Yazidi Kisan Gillar Kare Dangi


'Yan kabilar Yazidi.
'Yan kabilar Yazidi.

Wani jami'in Majalisar Dinkin Duniya, ya ce abubuwan da kungiyar Daular Islama ke aikatawa akan 'yan kabilar Yazidi 'yan tsirarun kasar Iraki.

Wani jami'in Majalisar Dinkin Duniya, ya ce abubuwan da kungiyar Daular Islama ke aikatawa akan 'yan kabilar Yazidi 'yan tsirarun kasar Iraki, tamkar wani yunkuri ne na neman yi musu kisan gillar kare dangi.

Mataimakin babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya, mai kula da al'amuran da suka shafi hakkokin Bil Adama, Ivan Simonovic, ya ce bayan ziyarar da ya kai kasar Iraki, ya na da shaidar dake nuna cewa 'yan tawayen na karkashe 'yan Yazidin dake kin shiga addinin Islama.

Mayakan Daular Islama sun kashe daruruwan 'yan kabilar Yazidi wadanda sunan su daya da addinin su, kuma sun kama daruruwan matan su da kananan yaran su mata.

A farkon makon nan jiragen saman dakon kaya na Amurka suka jefawa Kurdawa mayaka makamai da albarusai a arewacin kasar Syria, amma bayanai sun nuna cewa a kalla daya daga cikin lodin kayan da aka jefa ta jiragen sama ya fada hannun 'yan tawayen Kungiyar Daular Islama.

Wani bidiyon da 'yan kungiyar ta Daular Islama suka yi ya nuna wani mutumin su sanye da hular badda kama ya na duba gurnetoci, da albarusai da kuma rokoki.

Kakakin ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, John Kirby ya ce sojoji na yiwa bidiyon kallon kwakkwafi domin su tabbatar da sahihancin sa, kuma ya ce daga cikin lodin makamai 28 da aka jefa ta jiragen sama, ya na da yakinin cewa lodi 27 sun shiga hannun Kurdawa mayakan dake kokarin hana 'yan Daular Islama kama garin Kobani.

Da ma dai, tun ba yau ba, mayakan Daular Islama sun mallaki tulin makaman Amurka da suka kwace daga wurin sojojin Iraki da suka tsere lokacin da 'yan tawayen suka kama manyan yankunan kasar ta Iraki.

XS
SM
MD
LG